A ranar Talata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ya amincewa da yin amfani da kashi daya cikin kudaden da kasa ta tara da wadanda ta samu daga tallafi ga fannin kiwon lafiyar kasar nan.
Wannan shine karo na farko da gwamnatin Najeriya ke yin haka bayan amincewa da kudirin da majalisar kasa tayi a 2018.
Dokar kiwon lafiya ta hori gwamnatocin kasashen Afrika da su ware kashi daya daga cikin kudaden da suke tarawa duk shekara domin inganta fannin kiwon lafiyar su.
A yanzu haka gwamnatin Najeriya za ta biya Naira biliyan 55.1 wa ma’aikatar kiwon lafiya sannan gidauniyyar Bill da Melinda Gates za ta tallafa wa fannin da dala miliyan biyu wanda a yanzu haka dala miliyan 1.5 na cikin asusun ma’aikatan.
Sauran kungiyoyin bada tallafi daga kasashen waje kamar su ‘Global Financing Facility (GFF)’ za su tallafa da dala miliyan 20 sannan ‘Department for International Development (DFID)’ za ta tallafa da Fan miliyan 50.
Bayan haka shugaban kasa Buhari ya kuma kaddamar da shirin tallafa wa fannin kiwon lafiya na jihohi da suka nuna kwazo wajen ganin su inganta fannin kiwon lafiyar jihohin su.
Ya ce hakan na cikin kokarin da wannan gwamnatin ke yi domin ganin ta samar wa mutanen kasarnan ingantaccen kiwon lafiya ga kowa a kasar nan.
A nashi tsokacin ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya bayyana cewa gwamnatocin jihohi za su ware Naira miliyan 100 domin zubawa a wannan asusu domin ganin fannin kiwon lafiyar kasar ya ci gaba.
” Hakan zai taimaka mana wajen cin ma burin mu na inganta kiwon lafiyar mutanen musamman mata da yara kanana.
A karshe shugaban kwamitin kiwon lafiya na majalisar dattijai Lanre Tejuosho ya bayyana cewa majalisar na gab da kammala tantance kudirin samar da inshorar lafiya ga kowa a kasar nan.
Ya ce da zarar wannan kudirin ya zama doka samun inshoran kiwon lafiya da kula ga mutanen kasar nan zai zama dole.