YAJIN AIKI: Har yau ASUU da Gwamnatin Tarayya sun kasa cimma matsaya

0

Wani karin haske da ya bayyana a cikin tattaunawar neman matsayar da a ke ci gaba da yi har zuwa jiya Laraba tsakanin Gwamnatin Tarayya da Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa, ASUU, ya nuna cewa za a dau lokaci mai tsawo kafin bangarorin biyu su cimma amincewa da juna.

Kungiyar ta ce har yanzu babu wani abin-a-zo-a-gani daga bangaren gwamnatin tarayya wanda zai nuna cewa gwamnatin da gaske ta ke yi wajen kawo karshen yajin aikin da ya shafe watanni uku ana yi.

ASUU ta tafi yajin aiki ne tun a ranar 4 Ga Nuwamba, 2018.

Wasu daga cikin manyan bukatun da malaman jami’o’i ke neman a biya musu, su ne a cika musu alkawurran da aka daukar musu a jarjejeniyar 2012, ta 2013 da kuma ta 2017.

Dukkan ukun alkawurra ne da suka jibinci samar da kudaden inganta fannin ilimi.

Yarjejeniyar 2013, Gwamnatin Tarayya ta amince cewa jami’o’i mallakar gwamnatin tarayya su na bukatar naira tiriliyan 1.3 domin sake inganta su.

An amince za a biya kudaden kashi-kashi, wato za a biya naira bilyan 200 cikin 2013, 220 cikin 2014, 220 kuma cikin 2015. Sai 220 cikin 2016, naira bilyan 220 cikin 2017 da kuma wasu naira bilyan 220 cikin 2018.

Gwamnatin Goodluck Jonathan dai ta biya jami’o’in naira biliyan 200 a cikin 2013, amma daga nan ba ta sake biyan ko sisi ba.

Shekaranjiya Talata ASUU ta yi taro na bakwai da Gwamnatin Tarayya, amma babu wani abin kwarai a cewar ta da za ta iya komawa ta nuna wa sauran mambobi cewa ga shi an cimma a taruka shida na baya a aka gudanar.

Cikin farkon makon nan ne gwanatin tarayya ta ce ta ware wa jami’o’in naira biliyan 15.

Sai dai kuma shugaban ASUU, Biodun Ogunyemi ya ce wadannan kudade sun yi kadan da har za su nuna wa malaman jami’o’i har su amince cewa gwamnatin tarayya da gaske ta ke yi.

Share.

game da Author