Sojoji sun kashe ’yan bindiga 17, sun kama 67 a Nasarawa da Taraba

0

Rundunar Sojojin ‘Operation Wild Stroke’ da ke aiki a Nasarawa, Benuwai da Taraba, sun ce sun bindige wasu ‘yan bindiga har 17 kuma suka kama 67, a cikin watanni 8 da suka shafe suna aiki.

Haka kwamandan su Adeyemi Yekini ya bayyana a lokacin da ya ke magana da ‘yan jarida a Lafiya, jihar Nasarawa.

Ya kuma nuna wa manema labarai din makamai 45 iri daba-daban da albarusai iri daban-daban har 701 da ya ce an kwace a hannun ‘yan bindiga a sansanin su da tarwatsa a Zwere, da ke yankin Bassa, cikin Karamar Hukumar Toto, a jihar Nasarawa.

Kwamandan ya ce ba za su sarara ba har sai sun kawar da duk wasu batagari da suka addabi jihohin uku.

Share.

game da Author