Nyako ya roki mutanen jihar Adamawa su zabe dan sa na jam’iyyar ADC gwamnan jihar

0

Tsohon gwamnan jihar Adamawa Murtala Nyako ya roki mutanen jihar Adamawa su yi masa kara su zabi dansa AbdulAzeez Nyako da yake takarar zama gwamnan jihar a inuwar jam’iyyar ADC.

Nyako ya bayyana cewa dansa ne AbdulAzeez zai dawo da martabar jihar da gwamna mai ci Jibirilla Bindow ya yagalgala a idanun mutane.

” Lokaci yayi da mutanen jihar za su dawo daga rakiyar gwamna mai ci wato Jibirilla Bindow, jama’a su canja shi da dana na jam’iyyar ADC. A gwada jam’iyyar ADC.

” Bindow da jam’iyyar sa APC sun ba mutanen Adamawa kunya matuka domin kuwa babu wani abin azo a gani da gwamnatin ta tabuka a shekarun da tayi ta na mulki a jihar.

Share.

game da Author