Sabon Sufejo Janar na ’Yan sanda, Mohammed Adamu, ya bada umarnin a gaggauta ruguje Rundunar ’Yan Sandan Hana Fashi da Makami, wato SARS zuwa gida-gida.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN ya ruwaito cewa kafin wannan umarni, rundunar SARS ta na karkashin Hedikwatar ’Yan sanda ta kasa ce.
Dama kuma ba a dade da yi wa SARS kwaskwarima ba, biyo bayan korafe-korafen da ake yi wa rundunar na wuce-makadi-da-rawa da kuma sauran laifukan da suke amfani da kayan kakin su su ke aikatawa, musamman cin zarafin wanda bai ji ba bai gani ba.
Adamu ya bada wannan umarnin ne a lokacin da ya yi wata ganawa ta musamman shi da kwamishinonin ‘yan sanda da sauran masu manyan mukamai sama da kwamishina.
Ya ce daga yau Kwamishinan ‘Yan Sanda na kowace jiha shi ne zai kasance SARS da ke jihar sa su na a karkashin sa.
Ya ce su kuma SARS na Babban Birnin Tarayya za su kasance a karkashin Babban Mataimakin Sufeto Janar mai kula binciken manyan laifuka (FCIID).
Kuma ya ce daga yanzu duk wata bahallatsa ko barna ko zaluncin da SARS suka aikata, to kwamishinonin da SARS ke karkashin sun a jihohi da kuma na Babban Birnin Tarayya ne za a dora wa alhaki.
Ya kuma ruguza kwamitin binciken zargin zaluncin da ake yi wa jami’an SARS, ya ce DIG da SARS na Abuja Hedikwata ke karkashin sa, shi ne zai karbi aikin binciken zarge-zargen da kae yi wa jami’an SARS.
Discussion about this post