Shugaba Muhammadu Buhari ya kori Shugaban Hukumar Inganta Manyan Makarantu ta Kasa (TETFund), Abdullahi Baffa.
Sai dai kuma Buhari har ila yau ya maye gurbin Baffa da Sulaiman Bagoro, wanda ya kora cikin 2016, ya nada Baffa.
Sanarwar korar Baffa na cikin wata takardar bayani da kakakin yada labarai na Ma’aikatar Ilmi, Ben Goong ya sa wa hannu a yau Litinin.
Sanarwar ta ruwaito Ministan Ilmi, Adamu Adamu ya ce an kori Baffa, kuma Bagoro zai maye gurbin sa nan take.
Bogoro ya taba rike TETFund tsakanin 2014 zuwa 2016.
Baffa wanda kafin nada shi TETFund hadimi ne ga Ministan Ilmi Adamu, an nada shi ne a ranar 2 Ga Agusta, 2016.
Shi kuma Bagoro da aka sake nadawa, shi ya yi zamani da mulkin Goodluck Jonathan, wanda bayan Buhari ya hau, aka zarge shi da yin wala-walar naira biliyan 200 na kudin hukumar.
Ba a sani ba ko gwamnatin Buharin ta wanke shi daga zargin da ake yi masa kafin a sake nada shi a kan shugabancin hukumar a yau.