Yadda gobara ta cinye katafaren kamfanin barasa na Guinness kurmus

0

Wata gobara da ta tashi daga cikin jeji ta zagaya har cikin katafariyar masana’antar sarrafa barasa ta Guinness Nigeria Plc da ke garin Aba, a jihar Abia, inda ta kone masana’antar kurmus.

Jami’an kashe gobara sun yi iyakar kokarin da za su iya yi domin ganin zun kashe wutar, wadda ta tashi tun daga karfe 11 na safe, amma har sai da aka kai karfe 6:45 na yamma kafin a kashe ta.

Kamfanin Dillancin Labarai ya ruwaito cewa cikin abubuwan da suka kone kurmus, akwai dimbin kwalaben barasa, tulin sinadiran hada barasa, gine-gine da ofisoshi, kayan ofis da kuma kujeru da tebura, duk sun ci wuta.

Babban Kwamandan Kashe Gobara na Jihar Abia, Olezie Uche, ya ce jamai’an sa tare da gudummawar saurann ma’aikatan wasu masana’antun da ke kusa da wurin sun sha wahala sosai kafin su kashe gobarar wadda ta tashi a karshen makon da ya gabata.

Share.

game da Author