LA LIGA: Messi ya kafa babban tarihi a kasar Spain

0

Dan wasan kungiyar Barcelona ta Spain, Leonel Messi ya kafa babban tarihin da shi ne dan wasa na farko a tarihin gasar La Liga da ya fara cin kwallaye 400.

Messi ya samu cin kwallo ne ta 400 a wasan da Barcelona ta kara da kungiyar Eibar, inda Eibar din ta sha kashi da ci 3:0.

Wannan shekarar ce ta 13 da Messi ke buga kwallo a kungiyar Barcelona.

Daga tun da Messi ya fara buga kwallo, ya ci kwallaye sama da 600, ya ci kofin La Liga 9, Kofin Gwarzon Dan Wasa na Ballon D’Or 5.

Sai dai kuma har yau bait aba cin Copa America ban a Latin, kuma bait aba cin Kofin Duniya ba.

Share.

game da Author