Hukumar kwastam dake kula da shiyoyin jihohin Kebbi, Sokoto da Zamfara ta bayyana cewa ta tara Naira biliyan 1.8 a shekarar 2018.
Kakakin hukumar Kwastam na jihar, Magaji Mailafiya ya fadi haka wa manema labarai a garin Sokoto ranar Talata.
Mailafiya ya bayyana cewa hukumar ta iya tara wadannan kudaden ne a tsakanin watanni hudu a shekaran bara sannan hakan na nuna cewa hukumar ta sami karuwa a kudaden da take samu.
” Adadin kudaden da hukumar ta tara a shekarar 2017 ya kai Naira biliyan 1.4, amma a 2018 hukumar ta tara Naira biliyan 1.8.
Mailafiya ya kuma kara da cewa hukumar ba za ta yi kasa ba wajen ganin ta an hana shigowa da ababen da gwamnati ta hana shigowa da su kasar nan.
” A 2017 hukumar ta kama kaya da yakiai Naira miliyan 450, amma a 2018 hukumar takama kayan Naira miliyan 454.8.
A karshe Mailafiya ya yi kira ga mutane da su daina shigowa da abubuwan da gwamnati ta hana shigowa da.