Pogba ya yi wa Mourinho gwalo

0

Dan wasan tsakiya na Manchester United, Paul Pogba, ya gwasale tsohon mai horas da ‘yan wasan Jose Mourinho, wanda aka sallama, bayan da kungiyar ta fada rami gaba dubu.

Pogba ya yi wa Mourinho harara a duhu ne bayan da kungiyar ta yi nasara a kan Tottenham a gasar Premier na karshen makon jiya.

Pogba ne ya shirya wa Rashford yadda ya ci kwallo daya da aka yi nasara a kan Tottenham da ita.

“Ni din nan na fi jin dadin buga wasa da manyan kulob kulob da ke jin kan su. Kuma na fi son na rika kai hari, ba wai na rika tsayawa a tsakiya ina tare ko zama dan baya ba.

“Wannan sabon mai horas da mu ce min ya yi na daina tsayawa a tsakaiya ina badambadama, kamar yadda a baya aka rika dankwafar da ni.

“Ce min ya yi na rika kai hari a gaba kawai ba kakkautawa.” Inji Pogba.

Share.

game da Author