Kwadayin zama gwamna ba zai kai ni shiga kungiyar matsafa ba –Labaran Maku

0

Tsohon Ministan Yada Labarai a zamanin gwamnatin Goodluck Jonathan, kuma dan takarar gwamnan Jihar Nasarawa, a karkashin jam’iyyar APGA, Labaran Maku, ya bayyana cewa ba zai taba yin bata-bakatantan ba, har ya shiga kungiyar matsafa, saboda neman biyan bukatar zama gwamna.

Maku ya yi wannan furucin ne a lokacin da ya ke yi wa magoya bayan sa jabwabi, wadanda suka kai masa gaisuwar barka da shiga sabuwar shekara, a gidan sa da ke mahaifar sa, a kauyen Wakama, cikin karamar hukumar Nassarawa-Eggon.

“Tunda na taso ni dama da Ubangiji Allah na ke dogara, kuma ina ganin tasirin wannan imanin na wa a rayuwa ta.

“Tunda Allah ya taimake ni har na zama shugaban dalibai, na yi kwamishina, na yi mataimakin gwamna kuma na yi minista, don me kuma a yanzu zan saki igiyar imani na na shiga kungiyar matsafa don ina son zama gwamna?”

Maku ya shawarci shugabanni su rika isar da busharar zaman lafiya a cikin al’umma.

Daga nan sai ya yi alkawarin idan aka zabe shi, zai yi gwamnati wadda za ta tafi tare da jama’ar jihar baki daya ba tare da nuna bambanci ko bangaranci ba.

Share.

game da Author