Kungiyar Daliban Jami’a ta Kasa (NANS), ta fitar da shelar yi wa Gwmnatin Tarayya da Kungiyar Malaman Jami’a ta Kasa (ASUU) boren tayar musu da kayar-bayan yin zanga-zanga a dukkan fadin kasar nan.
Shugaban NANS na Kasa, Daniel Akpan ne ya bayyana haka a cikin wata takarda da ya fitar a ranar Lahadi.
Takardar ta bayyana cewa cikin wadanda za a shirya boren domin su, har da Kungiyar Malaman Manyan Kwalejojin Fasashe na Kasa (ASUP).
Akpa ya bayar da umarnin shirya zanga-zanga ta game-gari da ya ce su daliban jami’o’in kasar nan za su yi a ranarv 7 Ga Janairu.
Dama tun a ranar 23 Ga Disamba ne NANS ta yi barazanar gudanar da zangamin game-gari idan gwamnati ba ta gaggauta sasantawa da ASUU ba.
Kungiyar ta na mai nuna takaicin yadda an shiga wata uku kenan malaman jami’a na yajin aiki, tun daga ranar 4 Ga Disamba, 2018.
A gefe daya NANS ta yi tir da gwamnarin tarayya wajen kin nuna da gaske wajen kokarin shawo kan malaman jami’a su hakura su koma yajin aiki ta hanyar biya musu bukatun su.
A daya Gefen kuma kungiyar ta soki lamirin malaman wajen yin gaggawar ficewa daga taron sasantawa da gwamnatin tarayya, wadda ta furta cewa za ta biya musu kashi biyu bisa uku na bukatun na su.
Discussion about this post