Da munafikin Kirista gara zindiki wanda ba shi da addini –Inji Paparoma

0

Shugaban Mabiya Darikar Cocin Katolika na Duniya, Pope Francis, ya yi tir da halayyar munaficcin da ya ce wasu Kiristoci na nunawa a cikin ayyukan ibadar su.

Paparoman wanda ke a Fadar Vatican ta birnin Roma da ke kasar Italy, ta yi wannan tsokaci ne a lokacin da ya ke jawabi ga wasu dimbin mabiya a fadar sa, yau Laraba.

“Ta yaya za mu rika fama da wannan bahallatsa da wasu masu faman zuwa coci domin ibada a kullum ke tafkawa. Su na zuwa coci a kullum bayan sun fito kuma su ci gaba da rayuwar nuna kiyayya ga al’umma da kuma fadar munanan kalamai na batunci a kan wasu mutane?

“Ai gara ma ka daina bata lokaci ka na wahalar banza da sunan zuwa coci: Ka tsaya a zindiki maras addini zai fiye maka kawai.” Inji Paparoma.

Paparoma shi ne shugaban mabiya darikar Katolika, kungiyar addinin Kiristancin da ta fi sauran dariku yawan mabiya a duniya.

Yana da mabiya har kimanin biliyan 1.3 a fadin duniya.

Share.

game da Author