Kotu ta daure saurayin da ya yi wa ‘yar shekara 16 fyade

0

Kotun dake Yaba jihar Legas ta gurfanar da wani matashi mai suna Emmanuel Chukwu mai shekaru 22 da laifin yi wa ‘yar shekara 16 fyade.

Dan sandan da ya shigar da karar Thomas Nurudeen ya bayyana cewa Chukwu ya yi wa ‘yar makwabcin sa ‘yar shekara 16 fyade ranar 10 ga watan Nuwambar 2018 da karfe 11:30 na dare a gidan su dake lamba 16 layin Anthony Village jihar Legas.

Nurudeen yace bayan nan ya ja mata kune da kada ta fada wa kowa abin da ya faru.

” Chukwu ya dirka wa wannan yarinya ciki sannan bayan ita yarinyar ta fara ganin canji a jikinta sai ta fadi wa yayarta a gida.

Nurudeen ya ce bincike ya nuna cewa wannan yarinya ba ita ce kadai da Chukwu ke lalata da ba a unguwar su.

Chukwu ya musanta aikata haka a kotu.

A karshe alkalin kotun K.B. Ayeye ya bada belin Chukwu kan Naira 500,000 tare da gabatar da shaidu biyu dake biyan haraji a jihar Legas.

Share.

game da Author