Kotu ta daure matar da ta siyar da yara biyu, naira 450,000

0

A yau Laraba ne kotun Majiistare dake Minna jihar Neja ta gurfanar da wata mata mai suna Blessing Aluma da wani Oludare Prince da laifin siyar da yara biyu kan Naira 450,000.

Kotun ta kama Aluma da Prince da laifin siyar da yara.

Gunduma Ibrahim dan sandar da ya shigar da karan ya bayyana cewa Aluma mai shekaru 23 ta siyar da ‘yarta a kan Naira 200,000 sannan da ‘yar wata kawarta akan Naira 250,000 wa wata mata mai suna Nkechi dake zama a tunga Maje a Abuja.

Ibrahim ya kuma roki kotun da ta daga shari’ar saboda ‘yan sanda su sami nasarar gano bakin zaren wannan laifi tare da kwato yaran da Aluma da Prince suka siyar.

Alkalin kotun Fati Wushishi ta yanke hukuncin daure Aluma da Prince a kurkuku sannan za a ci gaba da shari’ar ranar 11 ga watan Fabrilu.

Share.

game da Author