Hukumar Yi Wa Kamfanoni Rajista ta Kasa (CAC), ta yi wa sabbin kananan kamfanoni da masana’antu har 39,074 rajista a cikin wata biyu kacal.
Shugaban Hukumar Azuka Azinge ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke jawabi a wurin wani taro a Lagos.
Ya ce wadannan kamfanoni an yi musu rajista ne tsakanin watannin Oktoba zuwa na Nuwamba, 2018.
Azuka ya ce an samu wannan nasara ce a dalilin sabon tsarin zabtare kudin yi wa kananan kamfanoni ko masa’antu kudin rajista.
Ya buga misali da cewa a da ana biyar kudin rajista har naira dubu 10,000.
Yanzu kuwa hukumar ta rage kudin zuwa rabi, wato maimakon a biya naira dubu 10,000, sai ake biyan naira 5,000 kacal.