Shugaba Muhammadu Buhari ya tabbatar da cewa zai duba batun rigingimun da ke tattare da batun lokacin ritayar Sufeto Janar na ‘Yan sanda, Ibrahim Idris.
A hirar da da jaridar Thisday da Arise TV, Buhari ya kuma dauki laifin kin sauya shugabannin hukumomin tsaron sa da bai yi ba tun cikin 2015.
Buhari na ci gaba da shan caccaka da zargi kwanan nan saboda kin sallamar shugaban ‘yan sanda, duk da rashin kokarin sa da ake gani da kuma cikar wa’adin aikin sa, tunda ya kai lokacin yin ritaya tun a ranar 4 Ga Janairu, 2019.
Ta kai wasu kungiyoyin gamayyar jam’iyyun siyasa barazanar yin zanga-zanga a ranar 15 Ga Janairu, matsawar Buhari bai sauke Idris dagac aikin dan sanda ba, tunda wa’adin say a cika.
A kan haka ne Buhari yace ai ba tsoron babban dan sandan ya ke ji ba, don haka zai dauki matakin da ya dace nan ba da dadewa ba.
“ Ni ma na gani a cikin talbijin, har wani na bani gargadi na karshe. Na yarda na dauki laifin. Amma dai zan dauki matakin da ya dace.
“Kuma bana jin a hada baki da shim un kafa ‘yan sanda kan titi mu na karbar hasafi daga masu mota, ballantana a ce idan na cire shi ba zai ba ni nawa kason ba.” Inji Buhari, a cikin raha.
Da ya ke amsa tambaya a kan kin janya shugabannin tsaro na sojoji, sai ya ce ya na duba lokacin da ya dace ne, domin shi ya na ganin ba daidai ba ne a canja shugabannin tsaro a lokacin da kasa ke cikin wani mawuyacin hali.
A batun sauya shugaban ‘yan sanda kuma, Buhari ya ce akwai da dama masu jira a nada su. Haka batun babban hafsan soja, Buhari ya ce mutum daya dai ne za a nada ko da mutum nawa ne ke jira..