WASKE WA NYSC: Kwanaki 100 bayan fallasa Minista Shittu, Buhari bai ce komai ba

0

An cika kwanaki 100 kenan tun bayan da PREMIUM TIMES ta fallasa yadda Ministan Sadarwa Adebayo Shittu ya ki tafiya aikin bautar kasa, bayan ya kammala karatun digiri din sa na farko.

Ganin yadda Shugaba Muhammadu Buhari ya yi rantsuwar yin aiki bisa adalci babu son rai da nuna bambanci, sai ga shi kuma har yau bai dauki matakin komai a kan Minista Shittu ba.

Ranar 20 Ga Satumba ne wannan jarida ta fallasa cewa Shittu bai je aikin bautar kasa ba.

Shi da kan sa ya tabbabar da haka, a cikin martanin da ya maida cewa bayan ya kammala jami’a sai ya shiga siyasa inda a cikin shekarar da ya kammala jami’a ne ya ci zaben majalisar jihar Oyo.

A kan haka ne, ya ce wancan wakilci a majalisa da ya yi a lokacin, shi ne madadin aikin bauatar kasa da bai je ba.

Wannan mataki da Buhari ya dauka na yin shiru a kan batun Shittu ne masu rajin kungiyoyin kare jama’a suka ce rainin wayo ne shi Buhari din ya ke wa ‘yan Najeriya, kuma zubar da mutuncin gwamnatin sa ne, wadda shi ya ke ikirarin cewa tsaftatacciyar gwamnati ce.

Haka ta faru ga wata minista kafin Shittu, wato Ministar Harkokin Kudade ta da, wadda ita ma PREMIUM TIMES ce ta fallasa ta.

Buhari bai dauki mataki ba, kuma har yau bai yi maganar ta ba, duk kuwa da cewa PREMIUM TIMES ta yi ta matsa lamba har sai da Adeosun ta yi murabus.

Haramta wa Shittu tsayawa takarar gwamnan jihar Oyo da jam’iyyar sa, APC mai mulki ta yi, ya tabbatar da laifin sa na nokewa ya ki zuwa aikin bautar kasa.

Dama kuma shugaban jam’iyyar APC ya shaida wa manema labarai, ciki har da PREMIUM TIMES cewa sun hana ministan fitowa takarar zaben fidda gwani ne, saboda ya ki zuwa aikin bautar ka.

Shugaban kungiyar rajin kare hakkin jama’a ta CISLAC, Auwal Rafsanjani, ya ce wannan halin ko-oho da Buhari ke yi ya na kau da kai a kan wani laifi da mukarraban sa suka yi, ya nuna cewa akwai wadanda gwamnatin Buhari ta raina, sai su ta ke bincika idan an zo batun karya doka, cin hanci yaki da rashawa.

Share.

game da Author