Sufeto janar Idris, ya fi kowane shugaban ‘yan sanda nuna bambanci a tarihin Najeriya – Saraki

0

Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, ya yi kaca-kaca da Sufeton ’Yan Sanda, Ibrahim Idris, ya na kari da cewa shi ne wanda ya fi nuna bambanci da son kai a tarihin shugabannin ’yan sandan Najeriya.

Ya yi masa wannan zargin ne bayan kokarin da jami’an tsaro su ka yi a baya-bayan nan na neman kama Sanata Dino Melaye.

Kakakin Yadac Labarai na Saraki, Yusuf Olaniyonu, ya bayyana a cikin takardar da ya fitar a madadin Shugaban Majalisar Dattawa, cewa kewaye gidan Dino Melaye da ‘yan sanda suka yi, a Abuja, shiri ne kawai domin a tauye kuma a toshe kaifin muryar da ‘yancin masu adawa da wannan gwamnati ta Buhari.

Saraki ya ce kewaye gidan Sanata Dino Melaye abin tsoro ne ainun dangane da yadda ‘yan sanda ke gudanar da aikin su a kan masu adawa.

Ya buga misali da yadda a kwanan baya Dino ya ce ‘yan sanda na kokarin kama shi da karfin tuwo, inda kwana daya bayan wannan furuci na sanatan, ‘yan sanda suka ce karya ne, babu wani shiri da suke yi na kama shi.

Saraki ya ce to ya aka yi kuma ko awa 24 ba a cika ba bayan ‘yan sanda sun ce ba su da wani shiri a kan kama Dino, sai kuma a ga dandazon jami’an tsaro sun kewaye gidan sa su na jiran ya fito su cafke shi?

Ya yi tir da yadda ‘yan sanda a cikin unguwar da Dino ya ke su ke katsalandan a batu harkokin ruwa da wutar lantarki da kuma yadda su ke cin zarafin masu himima a cikin gidajen unguwar cewa abin takaici da kunya ne, kuma ba za a amince da irin wannan karfe-karfar ba.

Saraki ya ce kawai dai kulle-kulle ne domin a hana Dino Melaye walwala a daidai lokacin da ake karakainar yakin neman zaben 2019.

Share.

game da Author