BOKO HARAM: Manyan Hafsoshin Sojan Najeriya sun sake garzayawa Maiduguri

0

Babban Hafsan Tsaro, Abayomi Olanisakin, tare da rakiyar Babban Hafsan Sojan Sama, Abubakar Sadique da Babban Hafsan Sojan Ruwa, Ibot-Ette Ibas, sun sake garzayawa Maiduguri a jiya Asabar, a cikin yanayi na halin rashin tsaron da yankin ke fama da shi.

Babban Hafsan Sojojin Kasa, Tukur Buratai ne ya karbe su a Maiduguri, wanda dama shi ya riga su zuwa jihar, tun bayan hare-haren bayan nan da Boko Haram suka kai.

Dama kuma cikin makon da ya gabata sai da manyan hafsoshin biyu suka kai ziyara a cibiyar sa-ido a kan tsaron da ke Maiduguri.

Olanishakin ya yi ganawar sirri ta sama da awonni hudu tare da sauran manyan hafsoshi da kuma kwamandan ‘Operation Lafiya Dole, da masu yi wa sojoji hoto da horas da atisaye, jami’an sojojin ruwa da kwamandojin sojojin sama.

Da ya ke yi wa manema labarai jawabi bayan kammala taron, kakakin rundunar sojoji, Sani Usman, ya ce ziyarar ba wani sabun abu ba ne, sun dai je ne domin su ga halin da ake ciki, bayan abubuwan da suka faru kwanan nan.

Ya ce dama ai Laftanar Janar Olanishakin ya sha zuwa ya na karbar rahotanni daga manyan hafsoshin sojan kasar nan da kuma kwamandojin da ke bakin fagen fama.

Ya gode wa sojoji da kuma jinjina musu wajen jajircewa da suka yi sun a fatattakar ‘yan ta’addar da suka rika kai hare-hare a kwanan nan.

Share.

game da Author