Shagari ya assasa gaggarimin ci gaba a Najeriya -Kungiyar Kwadago bayyana

0

Kungiyar Kwadago ta Kasa (NC), ta nuna alhinin rashin tsohon shugaban kasa Shehu Shagari, ta na mai bayyana irin gagariman nasarorin gudanar da ayyukan raya kasa da ya samar wa Najeriya.

NLC ta bayyana haka a cikin wani bayani da shugaban ta, Ayuba Wabba ya fitar jiya Lahadi, inda ya buga misali da kafa kamfanin tama da karafa da sarrafa man fetur.

Wabba ya kuma mika sakon ta’aziyyar Shagari ga iyalan sa da kuma kasa baki daya, wanda ya bayyana tsohon shugaban kasar a matsayin kamili kuma nagari na kowa.

“Ba don an kifar da gwamnatin Shagari a karshen shekarar 1983 ba, to da sai ya maida Najeriya cikin jerin kasashen da suka yi zarra a manyan masana’antu da ci gaban tattalin arziki.

Wabba ya nuna jimamin cire Shagari ta hanyar juyin mulki, domin bayan an tsige shi, gwamnatin sojoji ta mulkin Buhari ta tuhume shi, amma ba ta same shi da laifin komai ba.

NLC ta ce kungiyar ba za ta taba mantawa da Shagari ba, saboda shi ne ya shigo da dokar mafi kankantar albashi, inda ya kara albashi zuwa naira 125 a lokacin da, kwatankwacin dala 200 a wancan lokacin, cikin 1981.

Wabba ya ce Shagari shugaba ne da ya san muhimmancin leburan ma’aikaci, kuma ya san kimar dan adam.

Share.

game da Author