Makonni biyar kenan suka rage a yi zaben shugaban kasa, wanda za a kafsa tsakanin dan takarar jam’iyyar APC, Shugaba Muhammadu Buhari da kuma dan takarar jam’iyyar PDP, kuma tsohon Mataimakin SHugaban Kasa, Atiku Abubakar.
Amma da yawan mutanen kasar nan ba su ma san dalilin da ya sa Atiku ya fice daga aikin sa na jami’in kwastan ba, wanda ya yi ritaya shekaru 30 da suka gabata.
Atiku ya yi ritaya a ranar 30 Ga Afrilu, 1989.
Ya shiga aikin kwastan a ranar 30 Ga Yuni, 1969, a matsayin Mataimakin Sufurtanda.
Ya shiga aikin ne makonni kadan bayan ya kammala karatun Difiloma a Fannin Shari’a, a Jami’ar Ahmadu Bello, Zaria.
Ya fice ko a ce ya yi ritaya bayan ya shafe shekaru 20 ya na aikin kwastan, saboda haushin dankwafar da shi da aka yi aka ki kara masa mukami, saboda hassada da ganin-kyashi.
Sannan kuma a zuciyar sa ya na da muradin shiga siyasa. Don haka, sai iska ya tarad da kaba na rawa.
Ya shiga aikin kwastan ya na dan shekara 23, kuma ya shata wa kan sa matakai da shekarun da ya ke neman cimma burin sa na kaiwa kololuwar shugabancin hukumar kwastan baki daya.
“Na raya a rai na cewa idan na kai shekara 40 cif ban zama shugaban kwastan ba, to zan y i ritaya kawai daga aikin.
Haka Atiku ya fada a cikin wani littafin sa mai suna “The Story of Atiku Abubakar”, wanda marigayi Adinoyi Onukaba ya wallafa a cikin 2006, a lokacin ya na Mataimaki Na Musamman Na Atiku a Kan Yada Labarai.
Littafin ya na dauke da shafuka 338.
Atiku ya nemi shiga aikin soja a 1967, daidai lokacin da Yakin Basasa ya barke, dalibai a Zaria sun harzuka, suka rika yin zanga-zanga da kuma neman shiga aikin soja, haushin yadda kasar Faransa ta rika goyon bayan Biafra.
An rika yin zanga-zanga a Kaduna, har aka kama su Atiku, a lokacin ya na dalibi a ABU aka tsare su ofishin ‘yan sanda na dan takaitaccen lokaci, har sau biyu.
Bayan an kammala zanga-zanga, ya tafi barikin sosoji inda ake daukar sojoji, ya ce shi ma a dauke shi, amma sai aka ce sai wanda ya kammala karatu, ba wanda ke tsakiyar karatun sa kamar shi da bai kammala za a dauka ba.
Bayan shigar sa kwastan, tafiya ta mika inda har sai da ya shafe shekaru 18 a aikin kwastan sannan ya fara samun matsala.
A cikin wannan shekara ce aka nada shi mataimakin darakta mai kula da hana shigo da kwayoyi.
Atiku na daya daga cikin mataimakan darakta shida a hukumar kwastan, wadanda a cikin su ne idan darakta ya yi ritaya za a nada wani ya maye gurbin sa.
Shi kuma wanda ke kan mukamin darakta a lokacin, wato Shehu Musa, abokin Atiku ne na kusa, amma daga baya sai suka raba hanya.
Duk da cewa Atiku ya taka rawa wajen nada Musa mukamin darakta, wajen zuwa ya neman masa alfarma a wajen ministoci biyu na jamhuriya ta biyu, wato Ali Baba da Iro Abubakar Danmusa, sai Musa ya bari wasu fadawa suka kewaye shi, su na yi masa hudubar-shaidan cewa Atiku na nan ya na neman hawa kujerar sa ta darakta.
“An dankwafar da Atiku a mukamin har tsawon shekara 8, a matsayin Mataimakin Kwanturola. Atiku bai samu matsawa gaba ba, har sai da Musa ya yi ritaya.
“Daga nan ne aka yi masa karin mukami har sau uku, wato Mataimakin Kwanturola, Mai Taimaka Wa Kwanturola da kuma Mataimakin Darakta.
Ministan Harkokin Cikin Gida John Shagaya ne ya kara masa girma, bayan an damka masa kula da hukumar kwastan a lokacin da aka raba ta da Ma’aikatar Harkokin Kudade.
Daga baya an yi karin mukamai, inda kafin saukar John Shagaya ya mika sunan Atiku domin a ba shi mukamin daraktan kwastan.
Atiku ya ce ya yi tunanin zai samu mukamin, saboda ya cancanta, kuma Shagaya ya bai wa shugaba Babangida sunan sa a cikin wadanda za a kara wa girma.
Tafiya ta matsa, aka zo wata rana za a kara masa girma, amma sai wasu manyan tsohuwar jihar Gongola, suka je suka yi masa kafar-ungulu, suka hana a kara masa girma a wajen Babangida.
Sun ce wa Babangida wai akwai manyan jihar Gongola da dama a cikin gwamnati a lokacin. Wai idan aka kara wa Atiku girma, ‘yan wasu jihar za su yi bore.
A lokacin akwai Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Gambo Jimeta, Babban Hafsan Sojojin Sama Ibrahim Alfa, Ministan Ilmi, Jibril Aminu duk ‘yan Jihar Gongola.
A lokacin shi kuma Murtala Nyako na hankoron zama Babban Hafsan Sojojin Ruwa.
Wasu sun rika ganin Atiku ya kawo karfi a jihar Gongola, idan aka kara masa girma, to zame musu gagarabadau.
Daga nan sai Babangida ya saurari korafin su, ya nada Bello Haliru dan Jihar Sokoto a matsayin daraktan kwastan a lokacin.
Bello shi ne daga baya ya yi shugaban jam’iyyar PDP.
Tun daga lokacin a har Atiku ya yi ritaya, bai kara jin dadin aiki a karkashi ko tare da Bello Haliru ba.
Discussion about this post