An kori wasu ‘yan sanda su uku da aka kama da laifin yi wa wani matafiyi fashi da makami a Legas.
‘Yan sandan su uku sun yi masa dukan tsiya ne kuma suka kwace kudin san a saifa, kwatankwacin naira 221,508.
An kori su ukun da suka hada da Gbemunu Afolabi, Afolabi Oluwaseun da kuma Adigun Omotayo daga aiki saboda samun su da laifin fashi da makami.
Cikin makon da ya gabata PREMIUM TIMES HAUSA ta kawo maku labarin yadda ‘yan sandan suka yi wa matafiyin fashi da makami, bayan ya shigo Legas daga kasar Togo, da nufin ya zo hutu da kuma bikin Kirsimeti.
Kakakin ‘yan sandan jihar Legas, Chike Oti ya tabbatar da korar da aka yi wa jami’an su uku da ke aiki a ofishin ‘yan sanda da ke Dibijin na Ijanikin, Lagos.
Ya ce na hudun dan sanda sufeto ne mai suna Ameite, don haka am nika batun hukunta shi a hannun Ofishin Shiyya na Zone 2 domin su bada sanarwar korar sa.