PDP: ’Yan takarar gwamna biyu sun kaddamar da yakin neman zabe daban-daban

0

Wani sabon rikici ya kunno kai a cikin jam’iyyar PDP, yayin da a jiya Litinin ‘yan takarar gwamna guda biyu suka kaddamar da yakin neman zabe.

Buruji Kashamu da Ladi Adebutu duk su na irkirarin kowanensu shi ne sahihin dan takarar gwamna a karkashin PDP a jihar Ogun.

Ita dai INEC ta amince da sunan Kashamu, kuma shi ne ya kaddamar da na sa kamfen a garin Ijebu-Igbo, yayin da Adebutu kuma, wanda shi ne uwar jam’iyyar PDP ta kasa ta damka wa tutar amincewa takara, ya kaddamar da na sa kamfen a Abeokuta, babban birnin jihar.

Dukkan bangarorin biyu sun samu halartar dimbin magoya baya a wurin kaddamar da kamfen din.

Magoya bayan Kashamu na hakikicewa dan takarar su ne INEC ta amince a matsayin dan takarar gwamnan PDP a Ogun.

Su kuma magoya bayan Adebutu na cewa tunda dai dan takarar su ne jam’iyyar ta damka wa tuta, to hakan na nuni da cewa shi ne halastaccen dan takara, don haka Kashamu da magoya bayan sa na bata lokaci da dukiyar su ce kawai.

Dama su bangarorin biyu sun gudanar da zabukan fidda-gwani ne daban-daban.

Sai dai kuma ita INEC, ta yi amfani da hukuncin kotu ne ta ce Kashamu shi ne dan takarar da ta amince da shi, kamar yadda kotu ta yanke hukunci.

Share.

game da Author