A karo na biyar na zaman neman sasantawa tsakanin Gwmanatin Tarayya da kuma Kungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya (ASUU), bai cimma matsayar da ta sa malaman shawarar janye yajin aiki ba.
Malaman jami’o’in Najeriya sun shiga yajin aiki ne tun a ranar 4 Ga Nuwamba, suna neman gwamnatin tarayya ta cika musu alkawurran da sha dauka amma ba ta maida hankali wajen cika su.
Wannan ne karo na biyar na zaman sasantawa da aka yi, tun bayan fara yajin aikin.
Ba kamar zaman da aka yi na makonni biyu da suka gabata ba, a Hedikwatar Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ba, taron na jiya Litinin an gudanar da shi ne a Hedikwatar Ma’aikatar Kwadago da Inganta Ayyuka, domin nemo mafitar da za a tsaida yajin aikin wanda malaman jami’o’in ke yi, kuma babu ranar komawar su bakin aiki.
Yayain da ya ke magana da manema labarai, Ministan Kwadago da Ingantuwar Aiki, Chris Ngige ya ce an dage taron zuwa ranar 17 Ga Disamba.
Ya kara da cewa gwamnatin tarayya na korarin daukar duk matakan da suka wajaba wajen ganin ta magance dukkan bukatun malaman jami’o’in kasar nan.
Shi ma Biodun Agunbiyi, Shugaban ASUU, ya ce malaman jami’o’i da kungiyar su za su jira tukunna suka yadda ganawar da za su yi da gwamnatin tarayya a ranar 17 Ga Disamba za ta karke.
Discussion about this post