Mahara sun sake afka wa mutanen Birnin Magaji, sun kwashi abinci da dabbobi

0

Mahara dauke da makamai sun far wa kauyen Dan-Dambo dake karamar hukumar Birnin Magaji, jihar Zamfara inda a wannan karon har lalata da matan mutane suka yi da karfin tsiya.

Wani mazaunin kauyen Dan-Dambo ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa maharan sun far wa kauyen ne da misalin karfe 8 na daren Juma’a.

” Muna zaune ne kawai sai muka ji harbe-harbe ta ko-ina. Daga nan ne fa kowa ya fara gudun tsira. Mata ko da aka bari a gida wasun su sun sha dukan tsiya.

” Da zarar sun tambayeki ina kudi yake, idan kika ce babu sai su hau dukan mace. Wasu an ce har lalata sun yi da wasu matan.

” A haka ne fa suka rika kwashe tumakai da dabbobin da mutane suka mallaka. Sannan suka farfasa rumbuna suna dibar abinci.

Da suka gama abinda zasu yi sai suka kona inda suka fito.

Bayanai sun nuna cewa wasu da dama da suka gudu musamman mazaje sun gano iyalan su ne a kauyen Nasarawa Godal dake kusa dasu in da suka tafi neman mafaka.

Kamar yadda mazaunin ya bayyana, ya kara da cewa yanzu haka garin Birnin Magaji ne kawai yake da tsaro, shima wai don nan ne mahaifar ministan tsaro Mansir Dan-Ali.

Share.

game da Author