Kada ku amince da shirin Inshorar Lafiya da wasu jihohi suka kirkiro da shi – NMA

0

Shugaban kungiyar likitoci na Kasa (NMA) Francis Faduyile ya yi kira ga likitoci da su yi watsi da tsarin shirin inshorar kiwon lafiya da wasu jihohi a kasar nan suka fara.

Faduyile ya fadi haka ne a tattaunawar da mambobin kungiyar ta yi a makon da ya gayata a jihar Uyo.

Ya ce tsarin inshorar kiwon lafiya da wasu jihohin kasar nan suka fara ba shiri ne zai samar wa talakawa kiwon lafiya yadda ya kamata ba.

” Sanin kowa ne cewa an tsara shirin inshorar kiwon lafiya domin tallafa wa mutane da kiwon lafiya mai nagarta a saukake ne. Amma sai gashi wannan tsarin bata ware isassun kudaden da za a yi amfani da su domin Haka ba.

A dalilin haka Faduliye ya yi kira ga liktoci da su yi watsi da wannan shiri.

Ya ce likitoci za su amince da wannan shiri ne idan gwamnatocin jihohi sun amince su tanaji kudaden da ya kamata inshorn ta yi amfani da su.

Bayanai sun nuna cewa jihohin Legas, Delta, Bauchi, Abia, Anambara, Kaduna, Sokoto, Kwara, Kano da Imo na cikin jihohin da suka Fara wannan shiri.

Share.

game da Author