Zarcewar Buhari shine mafita ga kabilar ‘Yarbawa a kasar nan – Osinbajo

0

Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya ce kabilar Yarabawa ne za su bayar da damar Bayarabe ya yi shugabanci a 2013, idan suka zabi Buhari a 2019.

Osinbajo ya kada gangar wannan kabilanci a lokacin da ya gana da Alaafin na Oyo a garin Ibadan, inda ya ja kunnen Yarabawa su yi aiki domin ganin Buhari ya sake yin nasara a karo na biyu.

Ya ce idan Buhari ya yin nasara a 2019 zuwa 2023 Bayarabe ne zai yi shugabanci.

Idan kuwa Buhari bai ci ba, to ba a san rana ko shekarar da Bayarabe zai sake yin shugabancin kasar nan ba.

Osinbajo ya shaida wa Lamidi Adedibu cewa gwamnatin Muhammadu Buhari ta gudanar da muhimman ayyuka a kasar nan sosai da sosai.

Mataimakin Shugaban Kasa ya ci gaba da cewa faduwa zaben Buhari a 2019, to ko shakka babu faduwa zaben Yarabawa ne a 2023.

Share.

game da Author