Kungiyar ‘Advocacy in Child and Family Health at Scale (PACFaH@Scale)’ ta yi kira ga gwamnatin Najeriya da arika cire harajin Naira daya bisa ga kowani kira da mutum zai yi da wayar sa domin tallafa wa fannin kiwon lafiyar kasar nan.
Kungiyar ta yi wannan kira ne a taron inganta hanyoyin samar da kiwon lafiya mai nagarta wa mutane da aka yi a Abuja ranar Litini.
Shugaban kungiyar likitoci na (SOGON) Habib Sadauki ya bayyana cewa samar da ingantaciyyar kiwon lafiya wa kowa a kasa buri ne da kasashen duniya ke kokarin ganin ya tabbata.
Ya ce karban Naira daya domin inganta kiwon lafiyar mutane musamman talakawa zai yi matukar tasiri a kasa.
Bayan haka shugaban kungiyar mata ma’aikatan gidajen jaridu (WIM) Halima Ben-Umar ta yi kira ga sauran sassan gwamnati kan hada hannu domin ganin an cimma wannan buri.
Ta kuma ce samar da inshorar kiwon lafiya domin kowa a Najeriya na cikin hanyoyin da zai taimaka wajen samar da ingantaccen kiwon lafiya wa kowa a kasar nan.
A karshe shugaban kungiyar ‘Network for Nigerian NGCOs’ Ayo Adebusoye yace yin tanaji domin samar da kiwon lafiya mai nagarta wa kowa da kuma dakile matsalolin cin hanci da rashawa da ake samu wajen bada wadannan kudade zai taimaka wajen samun nasara bisa abin da aka sa a gaba.