Taron Matasa ‘Yan Takara: Yadda Ya Kaya a Ranar Farko

0

Taron wayar da kan matasa ‘yan takara taro ne da aka shirya domin wayar da kan matasa ‘yan takara game da siyasa da irin damar da suke da shi domin ci gaban kasa a siyasance da sannan irin rawar da za su iya takawa a farfajiyar siyasar Najeriya.

Cibiyar ‘Initiative for Advocacy, Growth and Advancement (YIAGA Africa)’ya shirya wannan taro da aka fara yau a garin Abuja.

A rana ta farko wato a yau litini an tattauna hanyoyin dabarun siyasa da yadda matasa za su iya yin tasiri a siyasar kasar nan.

Asusun bada Tallafi na kasar Britaniya UKAID ne suka dauki nauyin wannan gagarimin taro.

A bayanan da masu halartar taro suka yi,
Jami’ar gwamnatin kasar Ghana Oteng Mensah ta yi kira ga matasa musamman mata da su tabbata sun nemi sani matuka game da dokokin zabe.

Ta ce samun cikakken ilimi game da dokoki da yadda a ke gudanar da zabuka zai taimaka wa dan takara wajen kiyaye dokokin.

Daga nan sai mai wakilatar mazabar Tambal/Kabbe a majalisar wakilai na jihar Sokoto Abdulsamad Dasuki ya yi bayani game da matsalolin dake tattare da fitowa takara.

Bayan haka shugaban kungiyar ‘Founder of TechHer’ Chioma Agwuegbo ta yi kira ga matasa da su guje wa yin alkawaran da baza su iya cikawa ba.

Ta ce yin haka na daga cikin matsalolin dake hana dan siyasa tabuka abin a zo a gani a gwamnati sannan da zubar masa da mutunci a idonun wadanda yake wakilta.

A karshe shugaban kungiyar ‘234 crowdfunding’ Martins Hile ya yi magana kan hanyoyin da ‘yan siyasa za su iya bi wajen samun kudin kamfen.

Za a kammala wannan taro ne ranar Laraba.

Share.

game da Author