Bada da yawun mu Ango Abdullahi ya yi kalaman batanci ga Buhari ba – Kungiyar ACF

0

Kungiyar magabatan Arewa ACF ta nisanta kanta daga kalaman da shugaban kungiyar dattawan Arewa NEF, Ango Abdullahi yayi inda ya ragargaji shugaban Kasa Muhammadu Buhari da kalamai ma su zafi sannan ya soki salon mulkin sa.

An ruwaito cewa tsohon shugaban jami’ar Ahmadu Bello, dake Zariya kuma shugaban kungiyar dattawan Arewa NEF, Ango Abdullahi ya na cewa Buhari bai cancanci kuri’un ‘yan Najeriya ba a zabe mai zuwa.

Ango ya ce Buhari ya kasa cika alkawurran da ya dauka a 2015 a dalilin haka bai ga dalilin da zai sa kungiyar ta mara masa baya ba a zaben 2019.

Sai dai kuma kammala wadannan kalamai nasa ke da wuya sai ya fara shan luguden raddi daga wasu daga cikin dattawan kungiyar sa na NEF.

Wadannan ‘yan kungiyar sa sun fito karara suka nisanta kan su daga kalaman da Ango ya yi kan shugaba Muhammadu Buhari.

Sun bayyana cewa Ango furta wadannan kalamai a madadin kungiyar su ba, saboda haka kada a jingina su da Ango a wannan katobara da ya yi.

Anthony Sani, sakataren Kungiyar magabatan Arewa ACF, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi watsi da maganganun da Ango Abdullahi ya yi kan shugaba Mubammadu Buhari.

” Tun a jiya da ya fadi wadannan maganganu wasu daga cikin dattawa kamar sa dake wannan kungiya na NEF suka fito karara suka soki kalaman sa. Muma a ACF mun soki wadannan Kalamai kuma bama tare da shi farfesa a kan haka.” Inji Sani.

Share.

game da Author