Shugabannin Jama’iyyar APC na Jihar Ogun sun yi watsi da rushe su da Babban Kwamitin Zartaswa na APC na Kasa ya ce ya yi.
Jiya ne dai APC a karkashin shugabancin Adams Oshiomhole ta ce ta rushe shugabannin jihar Ogun da na jihar Imo, bisa zargin su da goyon bayan gwamnonin jihar, alhalin su kuma gwamnonin jihohin biyu ba su goyon bayan APC a jihohin su.
A jihar Ogun dai ba dan takarar da Gwamna Ibekunle Amosun ke goyon baya ne ya ci takarar gwamna ba. Wannan ne ya sa shi ya umarci dan takarar ta sa da sauran magoya baya su koma wata jam’iyya.
Ko da ya ke shi Amousun har yau ya na cikin APC, kuma ya tsaya takarar sanata.
Shugaban Jam’iyyar APC na jihar Ogun Derin Adebiyi, ya ce tatsuniya ce kawai da almara Adams Oshimhole da uwar jam’iyyar APC ke yi da ta ce wai ta ruguza su.
Ya ce shugabannin na APC ba su ganin girma da darajar dokokin kasa da dokokin jam’iyya, shi ya sa suke yin shisshigin da ke ta kara dagula APC.
Adebiyi ya ce don me su Oshiomhole za su yi katsalandan a cikin lamarin da ke a gaban kotu ana shari’a a kai.
Daga nan sai ya yi karin harke ya ce gaba dcayan rikicin APC a jihar Ogun fa ya na a gaban Babban Mai Shari’a na Babbar Kotun Abuja, Jude Okeke. Kuma babu wanda ya san bangaren da kotu za ta ba gaskiya da wanda za a ba rashin gaskiya.
“To don me idan banda ganganci da rashin bin dokar kasa da kuma raina kotu har wani zai azarbabin zartas da hukuncin rushe mu? Ya jira kotu ta zartas da na hukuncin mana?” Inji Adebiyi.