KANJAMAU: Masu dauke da cutar sun haifi ‘ya’ya 72 da basu kamu ba a jihar Bauchi

0

Shugaban hukumar hana yaduwar cutar kanjamau, tarin fuka, kuturta da zazzabin cizon sauro na jihar Bauchi (BACATMA) Muhammad Alkali ya bayyana cewa a shekarar bana iyayen dake dauke da cutar kanjamau sun haifi jarirai 72 da basa dauke da cutar.

Alkali ya ce an samu nasarar haka ne a dalilin kulan da wadannan iyaye ke samu a hukumar su na hana jariran kamuwa da cutar kanjamau tun suna cikin mahaifan su.

” Jariran da aka haifa duk suna cikin koshin lafiya.

Alkali ya jinjina wa irin goyan baya da tallafin da gwamnati ke ba hukumar. Sannan kuma da kokari da ta yi wajen hada masu dauke da cutar suka yi aure sannan ta ba su kula matuka har ya kai ga sun haifi ‘ya’yan.

Ya kuma yi kira ga mutane da su garzaya zuwa asibiti don sanin matsayin su game da cutar.

A kwanakin baya ne gidauniyar uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari ya shirya taro domin wayar da kan matan gwamnonin kasar nan bisa hanyoyin inganta kiwon lafiyar mata da yara kanana.

Taron ya gudana ne a gidan gwamantin jihar Edo inda Aisha ta hori mata kan daukan tsauraran matakan da za su taimaka wajen rage yawan mace-macen yara da mata a Najeriya.

Aisha ta ce rashin yin haka ne zai kara dulmuya kasar nan cikin matsalar mutuwar mata da yara kanana.

” A dalilin haka na ke kira ga kowace matan gwamna a wannan taro da ta maida hankali wajen wannan shiri.

Share.

game da Author