Za mu hada hannu da kasashen China da India domin hana shigowa da miyagun kwayoyi kasar nan- NAFDAC

0

Hukumar NAFDAC ta bayyana cewa za ta hada hannu da kasashen China da India domin ganin ta hana shigowa da miyagun kwayoyi musamman kwayar Tramadol kasa Najeriya.

Shugaban NAFDAC Mojisola Adeyeye ta fadi haka a taron wayar da kan matasa game da illolin yin ta’ammali da miyagun kwayoyi da NAFDAC da kungiyar masana magunguna suka shirya a Abuja.

Adeyeye ta ce yin haka ya zama dole musamman yadda shaye shayen miyagun kwayoyi ke neman ya cutar da rayuwar matasa a kasar nan.

” A binciken da muka yi mafi yawan mugan kwayoyin da ake shigowa da su kasar nan daga kasar China ne ko kuma India suke zuwa.

A makon da ya gabata ne shugaban hukumar(NAFDAC) Moji Adeyeye ta bayyana cewa hukumar za ta kona kayan da ta kama da ya kai Naira biliyan 198.

Adeyeye ta fadi haka ne a taron bukin cikan ta shekara daya da darewa shugabancin hukumar a Abuja.

Ta bayyana cewa cikin kayan da hukumar za ta kona sun hada da kwantinonin kwayoyin Tramado.

” Mun kuma kama kwantina 25 dankare da kwayoyin Tramadol da ya kai na Naira biliyan 1.7 kuma mun gurfanar da mutane uku da ke da hannu a harkar shigo da kwayoyin.

Bayan haka Adeyeye ta bayyana cewa a shekara daya hukumar ta biyan dukkan basukan da gwamnati ke binta da ya kai Naira biliyan 3.2.

Share.

game da Author