FYADE: Kotu ta daure dan shekara 14

0

A yau Talata ne kotun dake kasuwar Nama dake Jos jihar Filato ta daure wani matashi mai shekaru 14 da ta kama da laifin yi wa ‘yar shekara hudu fyade a kurkuku har na tsawon shekara uku.

Lauyan da ya shigar da karar mai suna Yakubu Audu ya bayyana cewa bayan ofishin ‘yan sandan Kaduna – Vom ta saurari karar daga mahaifin yarinyar Ezekiel Jatau ta aika da karan ga hukumar gurfanar da masu aikata laifi irin haka na jihar a ranar 24 ga watan Satumba.

” Jatau ya bayyana cewa wannan yaro ya danne ‘yarsa ne a daji bayan ya lallabe ta da wasa.”

Yaron ya nemi alfarmar sassauci daga kotu ganin cewa ya amsa laifin da yayi.

Alkalin kotun Lawal Suleiman ya daure wannan yaro a kurkuku na tsawon shekaru uku batare da beli.

Suleiman yace ya yi haka ne domin ya zamo ishara ga masu aikata irin haka.

Share.

game da Author