An kama dan takarar gwamnan Ogun da zabga karya a takardun sa

0

An kama dan takarar gwamnan jihar Ogun a karkashin jam’iyyar APC, Dapo Abiodun da zabga karya a cikin takardun karatun sa wadanda ya cike kuma ya aika wa Hukumar Zabe ta Kasa, INEC.

Abiodun wanda hamshakin dan hada-hadar harkokin man fetur da gas ne, ya na fuskantar zargin zillewa yak i zuwa aikin bautar kasa, irin wanda Tsohuwar ministar kudi, Kemi Adeosun da Minista Adebayo Shittu suka yi.

Takardun bayanan da suka shigo hannun PREMIUM TIMES sun nuna cewa Abiodun ya baddala bayanan sa wadanda ya bai wa INEC a lokacin da ya yi takarar sanata a zaben 2015.

Bayanan da ya bai wa INEC yanzu a zaben 2019 da ya fito takara, sun kauce kuma ba su yi daidai da wadanda ya bai wa INEC din a 2015 ba.

Shi ne dan takarar da ake zargi su Bola Tinubu da shugaban jam’iyyar APC, Adams Oshimhole sun daure wa gindi, ya kayar da dan takarar da Gwamnan Jihar, Ibekunle Imosun ya so ya gaje shi idan ya kammala wa’adin sa na shekaru takwas cikin 2019.

Wannan dalilin ne kuma Amosun ya raba hanya da uwar jam’iyyar APC, har ya yi rantsuwar zai taimaka a kayar da jam’iyyar a zaben gwamnan jihar.

Yayin da ake cikin wannan tata-burza, sai kuma ga bayanai da suka nuna cewa bayanan da Abiodun ya bayar wa INEC ka iya haddasa soke takarar sa gaba daya.

An tabbatar da cewa dan takarar na APC a zaben gwamna mai zuwa, bai je ya gudanar da aikin bautar kasa a lokacin da ya kammala jami’I’a ba.

Irin wannan dalili ne idan ba a manta ba ya sa APC ta hana Minista Adebayo Shittu fitowa takara, saboda bai je aikin bautar kasa ba.

Kakakin yada labarai na APC bai dauki wayar da PREMIUM TIMES ta buga mas aba, domin jin shi ma Abiodun za a janye takarar sa ne ko kuwa, ko kuwa za su jira su ga hukuncin da kotu za ta yanke tukunna?

AN MAKA ABIODUN KOTU

Wani mai suna Adesina Baruwa ne ya maka Abiodun kotu a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, inda ya nemi kotu ta gaggauta soke takarar sa, domin ya kantara wa INEC karyar cewa bai yi digiri ba, alhali kuwa ya yi digiri.

Dabarar da Abiodun ya yi wa INEC a wannan karo, sai bai ce mata ya yi karatun digiri ba, domin idan ya ce ya y i digiri, to tilas sai ya hada da kwalin shaidar aikin bautar kasa, wanda ya san bai je ya yi bautar kasar ba, a lokacin shekarun sa ba su kai na wanda ake yafe wa tafiya aikin bautar kasa ba.

A fam da ya cika a takarar sanata na zaben 2015, ya bayyana wa INEC cewa ya yi digiri a akan fannin kididdigar kudade, a lokacin ya na dan shekaru 29, cikin 1989.

Tunda cikin 1960 aka haife shi, tafiya aikin bautar kasa ya kama shi kenan.
A wani shafin sa na yanar gizo kuma an ce ya na da digiri a wani fannin can daban, a Jami’an Obafemi Owolowo. Amma kuma ba a ambaci shekarar da ya samu digiri din ba.

Shi ma Abiodun bai amsa kiran da PREMIUM TIMES ta yi masa ba, domin a ji ta bakin sa.

Share.

game da Author