A kara hakuri da ni a kara min lokaci – Buhari

0

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su ci gaba da hakuri da gwamnatin sa sannan su kara ba shi dan lokaci kadan domin ya iya isar da manufofin sa da shirin gwamnatin sa ga ‘yan Najeriya.

A yau Litini 17 ga watan Disamba ne Shugaba Muhammadu Buhari yaki bukin munar zagayowar ranar haihuwar sa.

Buhari ya cika shekaru 76 daidai yau.

A jawabin da Buhari yayi da luggar Hausa da Turanci, ya jinjina wa ‘yan Najeriya sannan ya yi kira ga re su da su ci gaba da hakuri da gwamnatin sa sannan a dan kara masa lokaci don ya samu ya isar da alkawuran da gwamnatin sa tayi wa jama’a

Bayan fareti da sojojin Najeriya suka yi wa shugaban kasa don karrama wannan rana Ministan tsaro, Mansur Dan-Ali, Shugaban ma’aikatan fadar shugaban Kasa, Abba Kyari duk sun mika wa shugaba Buhari Katin taya murna a madadin ma’aikatan fadar.

Share.

game da Author