KANO 2019: Akalla mutane Hudu ne aka kashe a kaddamar da kamfen din Ganduje

0

An ruwaito kashe mutane hudu a cikin mako daya kacal da fara kamfen na yakin neman sake zaben Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje.

An kashe mutanen a Kananan Hukumomin Bichi da Rano.

Ganduje, wanda aka kama dumu-dumu da kashe-mu-raba ta milyoyin daloli da ‘yan kwangila, amma ya musanta, ya fito ne a karkashin jam’iyyar APC a karo na biyu.

Ya fara kamfen din sa ranar Lahadi, 9 Ga Disamba, a garin Bichi, inda aka kashe mutum daya bayan ya sha sara da muggan makamai.

A gangamin Bichi, an kashe wani ne mai suna Sarki Yunusa da ke Kwanar Dumawa, cikin Karamar Hukumar Minjibir.

Ranar Asabar 15 Ga Disamba kuma, Ganduje ya sake jan zugar gangamin kamfen a garin Rano, inda a can ma ya bayar da tuta ga dukkan ‘yan takarar mukamai da ke Yankin Sanatan Kano ta Kudu.

PREMIUM TIMES ta gano cewa mutane uku da aka kashe a Rano, duk magoya bayan Mai Baiwa Shugaba Buhari Shawara ne a Harkokin Majalisar Tarayya, Abdulrahman Kawu, wanda ya yi takarar kujerar sanata a zaben fida gwani, tarecda Sanata Kabiru Gaya.

Ba a dai ce ga dalilin kisan na su ba, amma dukkan su an ce daga Karamar Hukumar Wudil suka fito.

Amma wani mai suna Adamu Danjummai, wanda ya ce wa PREMIUM TIMES shi kawun daga cikin wadanda aka kashe ne, mai suna Sale Kabiru.

Danjummai ya shaida cewa an binne gawar Kabiru, amma akwai wani kafcecen sara da takobi a kan sa.

Ya kara da cewa Kabiru ya rasu ya bar ‘ya’ya hudu da kuma mahaifiyar sa.

Wani da aka yi kashe-kashen a kan idon sa, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa masu gangamin taro duk arcewa suka yi a guje, yayin da ‘yan sanda suka fara harba barkonon-tsohuwa, domin kokarin kwantar da tarzomar da aka rika yi.

Ya kara da cewa da idon sa ya ga gawar mutane uku, kuma wasu da dama da aka ji wa raunuka, an garzaya da su asibitin garin Rano.

Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Fagge, Aminu Suleiman, ya halarci bizne gawar Yunusa, dan garin Kwanar Dumawa da aka kashe a Bichi a makon da ya gabata.

Da PREMIUM TIMES ta tuntubi kakakin yada labarai na rundunar ‘yan sandan jihar Kano, Magaji Musa, ya ce shi bai san abin da ke gudana ba, domin ya na hutun shekara-shekara, dawowar sa kenan ba da dadewa cikin jihar ba.

Share.

game da Author