An dakatar da Hakimai biyu saboda shirya taron yi wa Buhari addu’o’i a Jihar Gombe

0

Mai martaba sarkin Deba ya dakatar da wasu Hakimai biyu dake karkashin masarautar sa saboda gudanar da taron yi wa shugaban Kasa Muhammadu Buhari addu’o’i a garuruwan su.

Hakiman da aka dakatar sune, hakimin Garin Mallam Alhaji Julde da Ummaru Bappayo na garin Wajari.

A wasikar da sakataren masarautar Deba, Saidu Mele ya mika wa Hakiman, ba a bayyana dalilin da ya sa aka dakatar da su ba sai dai kawai an ce daga wannan rana su kwabe nadin su har sai sun ji daga masarautar.

” Daga yau an dakatar da ku daga ci gaba da sarautar garuruwan ku. ”

Julde ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa sukan gudanar da irin wannan zikiri da suka yi lokaci-lokaci domin yi wa shugabanni addu’o’i na musamman. ” Ni ban ga abin tashin hankali ba a ciki ba.” Inji Julde.

Julde ya kara da cewa yana da yakinin cewa gwamnatin jihar ne ta sa ayi musu haka.

Ita ko masarautar Deba karyata wannan korafi da hakiman suka yi tayi inda ta ce babu sarkin da ya dakatar da wani hakimi saboda wai ya shirya taron yi wa Buhari addu’o’i, su dai su bayyana laifukan su na gaskiya.

Shima Kwamishinan Yada Labarai na jihar Umar Nafada, ya bayyana cewa bashi da masaniya game da wannan zance na dakatar da wasu hakimai don sun yi wa Buhari addu’o’i.

Share.

game da Author