Kara kason fannin Ilimin kasar nan mafita ga ‘yan Najeriya – Minista Adamu Adamu

0

Minisatan ilimi Adamu Adamu ya yi kira ga gamnatin tarayya da na jihohi da su ware akalla kashi 15 daga cikin kasafin kudaden su na kowani shekara domin farfado da fannin ilimi.

Adamu ya ce ware kashi 15 bisa 100 daga cikin kasafin kudaden gwamnatocin jihar da tarayya zai taimaka wajen kawar da duk matsalolin da fannin ke fama da su.

Yawan adadin yawan yara da manyan da basu da ilimi a kasar nan baya raguwa sannan matsalolin rashin samun kwararrun malamai, rashin ingantattun kayan aiki da horas da malamai, yajin aiki da sauran su na cikin matsalolin dake kara gurguntar da fannin.

” Sannan dan kudaden da fannin ke samu takan kashe su ne a biyan albashin malamai da sauran aiyukka batare da ragowar komai ba domin inganta fannin.

Adamu yace a dalilin haka ne yake kira ga gwamnatocin tarayya da jiha da su ware kasha 15 bisa 100 daga cikin kasafin su domin farfadar da fannin ilimin kasar nan.

A karshe mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbanjo a nashi tsokacin ya ce ware isassun kudade da tsara ingantaciyyar shiri domin kashe wadannan kudade za su taimaka wajen inganta fannin. Ya ce a yanzu haka gwamnatin tarayya na kokarin ganin ta kara wani kaso na kudaden da fannin ilimin kasar nan ke samu daga cikin kasafin kudin ta na shekara.

Share.

game da Author