Abin da ya sa ake samun yawaitar tserewa daga gidajen kurkuku – NPS

0

Hukumar Kula da Gidajen Kurkuku ta Kasa (NPS), ta bayyana cewa rashin ababen more rayuwa da kuma tsananin azabtarwar da daurarru ke wa junan su a gidajen kurkuku, na daga cikin dalilan da ke sawa wasu ke balle kofa su na arcewa da karfi daga kurkukun Najeriya.

Kakakin Yada Labarai na Hukumar Kula da Gidajen Kurkuku, Francis Enobore ne ya bayyana haka, a cikin wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN), jiya Alhamis, a Abuja.

Enobore ya ce yawaita da kuma dalilan da ke sa daurarrru ke guduwa daga kurkuku a kasar nan, abin damuwa sosai.

Har ma ya kara da cewa wasu manyan dalilai kuma sun hada da cunkoson da gidajen kurkuku din suka yi dankam da jama’a.

“Misali, gidan kurkukun Fatakwal da aka gina domin ya dauki mutane 800 cif-da-cif, a yanzu akwai daurarru sama da 4,000 a cikin sa.

“Sannan kuma akwai babbar matsala inda ake gwamutsa wadanda aka yanke wa hukuncin dauri a wuri daya da wadanda ke jiran a yanke musu hukunci.” Inji shi.

Ya ce irin wannan babbar barazana ce, kuma ta na haifar da kara kangarewar mai karamin laifi, ta yadda idan ya fito, zai zama babbar barazana a cikin al’umma tagari.

Ya ce Babban Kwanturola na Gidajen Kurkuku, Ja’afaru Ahmed, ya bada umarnin a yi wa gidajen kurkuku kwaskwarimar gyaran da ya dace, domin a samu rangwamnen wasu matsaloli da ake fuskanta.

Ya ce ana ci gaba da yin wadannan gyare gyare a wurare sama da 70, domin tabbatar da cewa ba a sake samun tserewar daurarru daga gidajen kurkuku ba.

“Domin kara karfafa wa jami’ai gwuiwa, an kuma yi karin girma ga jami’ai 14,592.”Inji shi.

Share.

game da Author