An daure wasu da suka kashe dan sanda a garin Jos

0

Babbar kotun dake garin Jos ta daure wasu maza takwas da rundunar ‘yan sandan jihar ke zargi da yanke kan wani dan sanda kai.

Wadanda ake tuhuma sun hada da Abubakar Sani, Abubakar Mohammed, Hussaini Musa, Mohammed Zubairu, Abulahi Mohammed, Ibrahim Usman, Mohammed Doma da Sadiq Abubakar.

Ana zargin su da yanke kan wani dan sanda mai suna Yunana Ishaya a Otel din Gordons dake Farin Gada hanyar Zariya a karamar hukumar Jos ta Arewa.

Lauyan da ya shigar ta karan E.A. Inigbenoise ya bayyana cewa wadannan mutane sun aikata wannan ta’asa ne ranar daya ga watan Satumba.

” An kama su da layukan da suke amfani da su wajen yin saddabaru da aka kagara kama su da farko.

A karshe alkalin kotun A.I Ashoms ya yanke hukuncin daure su a kurkuku sannan ya daga shari’ar zuwa ranar 14 ga watan Disamba.

Share.

game da Author