Kungiyar Tarayyar Turai (EU), ta ce ta na goyon bayan Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, domin tabbatar da cewa masu nakasa maza da mata sun samu damar jefa kuri’un su a zabukan da INEC za ta gudanar cikin 2019.
EU ta bayyana haka ne a jiya Alhamis, lokacin da jami’an ta ke ganawa da manema labarai a ofishin kungiyar da ke Abuja.
An gudanar da taron manema labarai din ne, bayan wata ganawa a kebance da shugaban tawagar EU, Ketil Karlsen ya yi da shugaban INEC, Mahmood Yakubu da kuma wanda ya kafa Gidauniyar Tallafawa wa Zabaya, wato The Albino Foundation, Jake Epelle.
Karlsen y ace sun yi taron ganawar da Yakubu ne domin tattauna yadda za a shigar da masu nakasa su tabbatar da su ma sun yi zabe a 2019.
Ya ce tun tuni dama Tarayyar Turai ta dade ta na taimaka wa INEC, ba wai wani abu ba ne da kungiyar ta shigo da shi yanzu ba ana kusa ga fara zabe.
Karlsen ya kara da cewa tun daga 1999 Tarayyar Turai ta tallafa da sama da Yuro milyan daya wajen ganin an gudanar da karbabbe kuma sahihin zabe a Najeriya.
Shi ma Shugaban Kukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, Farfesa Mahmood Yakubu, ya jaddada alwashin da hukumar ta dauka na ganin cewa masu nakasa sun samu damar jefa kuri’a a zaben 2019 da sauran zabuka na gaba a kasar nan.
Discussion about this post