Mai Shari’a Mohammed Idris na Babbar Kotun Tarayya da ke Lagos, ya soke belin tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Kalu, bayan ya karya ka’idar beli ya fice daga Najeriya, ba tare da sanin kotu ba.
Idris ya ce ya soke belin da aka bayar na Kalu ne, wanda ke karkashin beli tun cikin 2007, a bisa sharadin cewa ya ajiye fasfo din na fita waje a kotu, idan zai fita waje domin wani uziri, ya nemi izni a ba shi ya fita.
Sai dai kuma a cikin makon da ya gabata, an ci gaba da sauraren shari’ar tsohon gwamnan, amma bai samu halartar kotun ba, bisa dalilin cewa ya fita waje neman magani.
Mai shari’a ya ce babu wanda ya fi karfin karya doka ba a hukunta shi ba, duk karfin arzikin sa kuma duk karfin mulkin sa, musamman kuma dokar nan umarnin kotu ce.
Kalu wanda ya yi gwamnan jihar Abia tsakanin 1999 zuwa 2007, ana yi masa tuhuma har guda 39 da suka jibinci zargin salwantar kudade.
Cikin makon da ya gabata, EFCC ta yi wa kotu korafin cewa Kalu ya yi tafiyar sa kasar Jamus ba tare da neman izni daga kotu ba.
Lauyan EFCC Rotimi Jacobs ya ce abin da Kalu ya yi, wani shiri ne ya kulla domin kawo tsaikon ci gaba da shari’ar sa.
Sai dai kuma lauyan tsohon gwamnan mai suna Awa Kalu, ya shaida wa kotun cewa likitocin da suka yi wa Orji Kalu tiyata ne suka bada shawarar ya zauna can har sai ya murmure tukunna kafin ya dawo Najeriya.
Mai Shari’a a makon da ya gabata ya bai wa Kalu wa’adin mako guda ya bayyana a kotu.
Kin bayyanar sa a kotun a jiya Litinin ne ya sa Mai Shari’a ya soke belin sa, kuma ya umarci da ya dawo ya kai kan sa ga hukumar EFCC, tare da takardun fitar sa kasashen waje da suka kunshi har da biza da fasfo.
Kotu ta bai wa EFCC umarnin cewa idan ya dawo bai kai kan sa ofishin hukumar ba, to ta gaggauta damke shi ba da wani bata lokaci ba.
An dage shari’ar zuwa ranar 23 Ga Janairu, 2019, ranar da za a ci gaba da tafka shari’ar a kullum.