Hukumar Kwastam Mai Sintirin Musamman da ke Shiyyar C, ta kama harsasai 4,375, bindigogi 2 da kuma rigunan sulken kayan sojoji saiti 200.
Wannan shiyya har ila yau ta kama buhunan shinkafa 430 da kudin su ya kai naira milyan 9 da kuma kwalaben kodin 1,160 da kuma fakiti 300 na kwayar maganin taramadol.
Shugaban jami’an sintiri na shiyyar, Kayode Olusemire ne ya bayyana haka, kuma ya ce an kama mutane uku da ake zargi da ya ce za a gurfanar da su a kotu.
Olusemire ya ce an kama kwayoyin maganin da kayan sojoji a Anacha, yayin da su kuma harsasai aka kama su a Enugu.
Ya ci gaba da cewa an kama buhunan shinkafar a Fatakwal.
Ya gargadi jama’a da cewa su guji aikata fasa-kwauri, domin sun san dai gwamnati ta haramta shi, kuma ya nuna takaicin cewa duk da kokarin da hukuma ke yi wajen ganin an kawar da shaye-shaye a kasar nan, wasu batagari sai kara daure wa harkar gindi suke yi ta hanyar shigo da miyagun kwayoyi cikin kasar nan.
Ya kara nuna takaicin yadda ake shigo da makamai, ya na mai hamdala da cewa ba don kwastan sun kama harsasan ba, to za a yi amfani da su ne wajen aikata mummunar ta’asa.