Matar aure mai suna Beauty Odinye ta roki kotun Mapo dake Ibadan da ta bata damar janye karar da ta shigar na a raba ta da mijinta ko ta halin kaka baya.
Beauty dai ta maka Nathanile a kotu saboda rashin kula da ita da ‘ya’yan ta da baya yi shekaru 12 kenan da auren su.
Beauty ta roki kotu da ta hakura sannan ta janye karar da ta shigar bisa cewa dama can karya ta ke yi wa mijin ta.
Shi ko mijin nata, wato Nathaniel ya bayyana wa kotu cewa sam bai yadda da wannan roko na matar sa ba, tunda tace bata son sa kuma, kotu ta raba kawai.
A karshe dai alkalin kotun ya nemi su sasanta a tsakanin su.