Shugaba Muhammadu Buhari ya gwasale jam’iyyar APC da shugabannin ta, inda ya kara jaddada cewa duk wanda aka yi wa ba daidai ba ko ya ke da korafi kan zaben fidda-gwanin jam’iyyar to ya garzaya kotu ya nemi hakkin sa.
Wannan wani raddi ne Buhari ya yi ga shugabannin jam’iyyar, wadanda suka yi gargadin cewa duk wani dan jam’iyyar mai korafi, to ya janye karar da kai a kotu, ko kuma ita jam’iyyar ta dauki mataki a kan sa.
“Ba za mu iya danne wa jama’a hakkin su ba. Mun kulla yarjejeniyar amincewa cewa za a gudanar da zaben fidda-gwani ta hanyar ‘yar tinke, wato kato-bayan-kato, ko kuma ta hanyar wakilan jam’iyya, wato ‘delegetes’, ko kuma ta hanyar inda masu takara suka cimma yarjejeniyar janye wa wani.
“Don haka idan har wani ya na ganin an bi ta wata hanya ko wasu hanyoyin da ba daya daga cikin wadannan ukun ba, aka danne masa hakkin sa na tsayawa takara, to zai iya tafiya kotu neman hakkin sa.
“Amma dai ni ba zan amince jam’iyyar APC ta haramta kotu a kan ido na ba.” Inji Buhari.
Cikin makon da ya wuce ne jam’iyyar APC ta bakin kakakin yada labaran ta, Lanre Isa, ya gargadi dukkan ‘yan jam’iyyar da suka garzaya kotu da su janye kararrakin da suka kai, ko kuma a dauki mataki a kan su.
APC dai ta shiga rikici tun bayan kammala zabukan fidda-gwani a fadin kasar nan, wanda aka yi zargin cewa tun da aka fara siyasa a Najeriya ba a taba yin harkalla a zaben fidda-gwani a fadin kasar nan, kamar na APC ba, daga matakin majalisar jiha, tarayya, sanatoci har ma da ‘yan takarar gwamna.