Kwamishinan kananan hukumomin jihar Zamfara Bello Dankande ya bayyana cewa babban dalilin da ya sa gwamnati ta dakatar da wasu hakimai hudu a jihar shine zargin da take musu da hannu a ayyukan ta’addanci a jihar.
Hakiman da aka dakatar sun hada da hakimin Gora dake karamar hukumar Talatan Mafara, da hakimin Barikin Daji.
Sannan akwai kuma hakimin Gyado da Tungan Dutsi dake karamar hukumar Bukuyum.
Dankande ya ce dukkansu za su bayyana a gaban kwamiti domin wanke kansu daga wannan zargi da ake musu.
Ya kara da cewa duk wanda aka samu da laifi zai dandana kudar sa sannan za a cire shi daga kujerar sarauta da yake kai.
Discussion about this post