Ganawar ASUU da Gwamnatin Tarayya bai kawo karshen yajin aikin malaman jami’o’i ba

0

Taron ganawa domin tattaunawa tsakanin Gwamnatin Tarayya da Shugabannin Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU), bai samar da mafitar janye yajin aikin da malaman ke yi ba.

An gudanar da tattaunawar ce jiya Litinin a Abuja, ba tare da an cimma wata kwakkwarar yarjejeniya ba.

Taron wanda aka fara shi wajen karfe 5:30 na yamma a Hedikwatar Ma’aikatar Ilmi, an karkare shi ba tare da an ci nasarar shawo kan shugabannin malaman na jami’o’i su hakura su janye yajin aiki ba.

Da ya ke magana da manema labarai bayan kammala taron, shugaban ASUU, Biodun Ogunyemi, ya ce har yanzu ana ci gaba da tattaunawa kenan za a ce, domin an amince nan gaba za a sake aza wata ranar da za a sake zaunawa.

Share.

game da Author