Mataimakin Gwamnan Kaduna ya gargadi shugabannin Kiristoci masu yi wa mabiyan su ‘hudubar karya’

0

Kiristoci manyan jami’an gwamnatin Jihar Kaduna, karkashin jagorancin Mataimakin Gwamna, Barnabas Bantex, sun yi kira ga shugabannin addinin kirista da su juji watsa jita-jita a cikin mabiyan su.

A cikin wata sanarwa da suka aiko wa PREMIUM TIMES da yammacin Alhamis, Bantex ya yi zargin cewa wasu shugabannin addini Kiristoci na jihar su na yada karairayi a cikin mabiyan su, ta hanyar alakanta kisan da masu garkuwa da mutane suka yi wa Sarkin Adara, cewa gwamnati ce ke da hannu wajen kashe shi.

Cikin sanarwar, Bantex ya ce sun yi wani taron gaggawa, wanda ba su taba yin irin sa ba, domin babu bukatar yin irin taron, saboda ba a bisa doron nuna bambancin addini aka kafa gwamnati ba, ko kabila ko jinsi.

Ya ce sun yi taron ne domin su tattauna batun barazanar da zaman lafiya a jihar Kaduna ke fuskanta, duk da cewa gwamnatin Nasir El-Rufai ta yi kokarin kwantar da rikicin ainun.
Ya kuma nuna cewa:

“Maganar gaskiya, mu na cike da mamakin yadda wasu fasto-fasto ke ta yada kalamai na kiyayya tare da da ruruta wutar fitina da kokarin harzuka mutane sake tayar da zaune tsaye, wanda hakan zai iya sake haifar da barkewar mummunan rikici.

“To ba fa za mu aminta da masu rura wutar fitina a cikin al’umma ba, ko da kuwa addinin mu daya da su.

“Mun yi mamakin yadda wasu shugabannin coci-coci suka wofintar da imanin su ta hanyar watsa kalamai na fitina da rura wutar mummunan rikici a Jihar Kaduna. Abin takaici ne kwarai da bacin rai irin yadda muka ganin wasu faya-fayan bidiyon da aka rika yadawa, inda wadannan masu kiran kan su fasto ke ta tunzura mabiyan su.

“Baya ga tunzura mabiyan su da cewa wai dokar hana fita a yankin da kiristoci suke zaune kadai ta shafa don a kuntata musu, fastocin sun kuma wuce-gona-da-iri, ta hanyar kantara wa gwamnatin jiha karyar cewa ta na da hannu wajen kisan Agom na Adara, Maiwada Galadima. Don haka kalaman da suke furtawa na dalilin kisan basaraken, abin dubawa ne ga jami’an tsaro.

“A matsayin mu na manyan kiristoci da ke cikin wannan gwamnati, mu na karyata wadannan karairayin na su da cewa:

– A ranar da aka yi garkuwa da Agom na Adara, ba daga wurin halartar taro tare da Gwamna ko wani jami’in gwamnati ya ke ba.

– Gwamnati da jami’an tsaro sun yi bakin kokarin su domin ganin an saki basaraken daga hannun wadanda suka yi garkuwa da shi.

– Agom na Adar aba shi da wani sabani da gwamnatin jihar Kaduna a kan batun tankiyar wata sarauta. Sannan kuma babu wani shiri da ake yi wai domin a musuluntar da yankin. Mu na kira ga masu ruruta wannan fitina su daina, kuma su sani wannan cin fuska ne ga mu kiristocin da ke cikin wannan gwamnati.

– Wannan gwamnatin ce ta nada Mrs. Victoria Galadima, matar basaraken mukamin Babbar Sakatariya.

– An kafa dokar hana fita a kowane yanki, kuma ana tsaurara doka ne saboda irin mummunan kashe-kashen da ya barke. Domin haka ne kawai zai iya shawo kan rikicin. Kuma zama cikin dokar hana fita, ya fi alheri bisa ga afkawa cikin kashe-kashen da babu dalili. Ko a lokacin rikicin 2016 da 2017, ai an sa dokar hana fita a yankin da rikicin ya fi shawa kawai.

– Akwai wani bidiyo da wannan fasto ke nuna alakar sa da wadanda ke da hannu a rikicin. Aikin jami’an tsaro ne su gudanar da bincike a kan sa.

Yayin da ya ke kara nuna fushin sa da yadda aka alakanta kisan Maiwada Galadima a kan gwamnatin jihar Kaduna, Bantex ya kuma yikira da a zauna lafiya, a kauda kunne daga sauraren hudubar shaidan da wasu baragurbin fastoci masu neman haifar da fitina ke wa mabiyan su.

Share.

game da Author